*** *BARIKI IYAWA PART 15* ***
*** *BARIKI IYAWA PART 15* ***
.
Parlour yai,kamshi yaji ya karade gida,ga nan kofar glass
din parlourn Sa'an a bude,,ya lumshe ido yana shakar
kamshin,,gudu gudu,Sauri sauri ya karasa saman nata,,bata
parlour, sai yai daki,Halamun kashe shawer yaji,Ko'ina sai
kamshi ke tashi,a gadon ya kishin gida tare da jawo rigar
baccin data cire kan ta shiga wanka yana shaka,,Ta bude
kofa,daure da Towel babba,, har ga Allah ta tsorata, dan
bata ji bude kofar shi ba,A razane take kokarin komawa
bandakin kan ya kira ta,, Towal har yana kokarin kunce
wa,,Gaban ta ya fara dukan uku uku,,Da sauri ta rintse ido,
kawai haushi ma ya bata,,Sai fa tayi da gaske wannan
kishin Hafeez din kar yai mata cikas,Jawo ta yai,bama
ruwan shi da lemar dake jikin ta, harda sakar ajiyar zuciya,
Da sauri ta nemo hankalin ta ta fara kiciniyar zame wa,sai
dai ina,ya kara kan kame ta,"Ka rufan asiri Fa Baby,,.
Wallahi ba ruwa na,,ya dan sassauto ta,"Gaisa wa fa nazo
muyi,ko ya Haram ta,da sauri ta daga mishi kai,,.."La'ila
Ha'illalahu,,..Da sauri Suka juya jin muryar Zahra,,kallon
Hafeez take da tuhuma,dan ita a zaton ta daga badaki
suke,dan duk jikin shi ya jijike da ruwan jikin Sa'an,, Ta
maka wa Sa'a harara,,"Haka zamuyi da dake??,..Ni zaki
gwadawa BARIKAN ci ranar kwana na,,. "ke dan Allah ya
isa,mey ta miki na BARIKI??,.. Ba tasan lokacin da Shima ta
maka mai harara ba tana hawaye," Nidai aka shiga hakkina
Wallahi ban yafe ba,,tai kasa tare da mako musu kofa..Sa'a
ta dau hijab tana kokarin sawa ya rike,,Da sauri taci
mur,,"Ina kwana,,,kaje pls yanzu zan sakko,.ka kuma
rarrashe ta,dan baka kyauta ba,,Yai dan karamin tsaki,,"Mey
nai ne Wai tukun??Ta karbe hijab din ta,"kaje zan fada
maka inna sakko,abinci na dining,,Ta fara janshi a hankali,
yana kaiwa tsakiyar parlourn ta juya da gudu ta rufe
kofa,,.Toh mey suke nufi dashi??Suna nufin sun fishi sanin
addini da adalci kome??.
.
Yai kwafa,tare da sakkowa kasa,,. Dakin Zahran ya nufa,ta
hada kai da gwiwa sai nadar kuka take,ya zauna a bakin
gado abin na bashi mamaki,Toh mey yai na kuka har
haka??..Dan ya taba Matar shi shine ya shiga hakin nata
komai??..Yadai daure yace"Yanzu Zahra dan abun nan
danayi ne har na chan chanci kimin fitsara?,,Tuni ta kara
kuluwa,,"Au,dan abu ma ka dauke shi??,,wato dan kaga ina
bacci shine zaka silale harda zuwa ka mata wanka??..Da
sauri ya dago,."Wanka kuma? ke bana son shirmen nan naki
fa,,.Gani kikai mun fito a bandakin komai??ta kada
kai..yace"Toh ban son zargi,,Gaisuwa kawai naje muyi,,.A
ranta tace"Oho,dan tsabar BARIKI ne yasa ta rungume shi
kenan?.. Badan na shigo ba Allah ne yasan abun da zata
mai,,Ta goge hawayen ta,,duk da haka bata gamsu ba sai
da tace"Amma ran kwanan ta ni Ai sai 10 ko 11 nake ganin
ka,,Ya girgiza kai,, Ashe haka mata biyun suke??..Tab,shi
kam bamai sa mishi Tension,,.
.
"Zan gyara Toh, ki shirya kizo Dining muyi break,,yai waje
bai jira mey zata ce ba,Da azama tai bandaki tai brush ta
dan watsa ruwa, powder kawai ta mitsika,,. Dakyar ta
tattara nutsuwar ta ta Shafa mai da dan light make up,, sai
dai tai kyau,,ta feshe turare masu kamshi kan ta zabo wata
shadda milk mai dan laushin jiki,tasha aiki da zare brown
da stones, Riga da skirt ne,ta danyi dauri a saukake single,
ta sake fesa turare,,,ta kalli mirror kayan ya kamata,tai
murmushi kan ta fito parlour,, Dai dai shi kuma ya fito a
dakin Zahra,,Ya Ilahee,, Rokon Allah take ya saukaka mata
kishi.,, Kallon ta yake yadda take wani rausaya kamar bata
son taka benen, murmushi ta sau mishi da taga ya dan
harare ta,, wato fishi shi adole yayi??Ta ja mishi kujera,ba
musu ya zauna,.kan itama taja ta zauna,,ta daura hannun ta
a kunne halamun " Sorry?Yadda ta langwabe kai bai San
sanda ya sau fuska ba,,Ya kai hannu zai kama hannun ta,da
sauri ta zame,Tana dan dariya kadan tace mishi"Kai Baby
mu akwai Neman fada,,ya dan harare ta kadan,,Tai
murmushi, "Allah ni na yafe gaisuwar nan taka nan
gaba,,zan na sakkowa mu gaisa,,Ya kara hararar ta,,. Tai
murmushi,, yace" Toh ni ban yafe ba, Ba wacce nake
tsoro,,Tace "Toh,it's Ok,,Bazamu kuma ba,amma kaima ka
kiyaye mu,,Ya dungure mata kai,,Dai dai Zahra ta
fito,,.Turus ta tsaya,,ita kam mey zatai wa Matar nan ne ta
fita har kar ta??..Tai kwafa kan ta karaso,,Kujera ta ja ta
kusa dashi ta zauna,ta dallah wa Sa'a harara,.ita kwa sai
tai mata murmushin Da yafi komai ci mata rai, wannan
munafukin murmushin Sa'an ba karamin tsanar shi tai ba,,"
Sis ina kwanan mu??Ba kunya ta amshe,,ta juyo kan
Hafeez da wata murya tace"Baby An tashi lafiya??Ya yage
baki,, "Lafiya Unique,, Da sauri Zahra tace" Au,Ina kwana
Yaya?,,Sa'a ta kunshe dariyar ta,kai Lalle wannan Baho ce
amma??Ya kallo ta da mamaki,,Ashe fa ko gaida shi batai
ba koh??Ya kada kai, "Lafiya lau,,Ya kuka tashi??
.
Zahra tadan harare shi cikin wasa,"sai yanzun zaka San ya
na tashi Fisabilillahi Dear??Suka zuba mata ido shida Sa'a,,
ta cigaba cikin gwalli," Dakyar fa nakai kaina bandaki,, Ta
kallo Sa'a, ganin yadda take kallon ta yasa ta cigaba da
fi'ilin ta,ita adole zata bawa kishiya haushi,,bata San bada
kanta take ba,..Banza Yai da ita yana zuba Tea,,Tuni
zuciyar Sa'a ta fara tafarfasa,,amma ko a fuska bata sake
ta gane ba, sai ma murmushin kara tusa bakin ciki da take
mata,, Amma dan ta kashe zancen yasa tace "Toh kiyi
serving namu gashi Baby na jin yunwa,.ta harare ta kadan
kan ta fara zuba wa Hafeez din,,da in ranshi yai dubu ya
baci..Ganin bata zuba mata ba yasa ta jawo ta zuba,ta
hada tea Baki kawai,,Ya kallo ta, murmushi ta sau
masa,Tuni kwa ta yaye mishi kunci,,duk loma 1 sai ya kallo
ta,, Sai kwa ta sau mishi murmushi, shaf sun manta da
Zahra,,. Tsaki tai,ta tashi tai kitchen,indai dan ta mata break
ne toh ita zatai launch din ta,yar BARIKI kawai,.Ai kamar
jira yake ta kauce ta fara bashi a baki,,,Gogan ya ware
harda zuba musu pic,,Tace suje kitchen su Taya sis aiki,ba
musu ya bita,sai ganin su tai suna dariya, Sa'a tace"
Sis,dame zamu tayaki??tai mata kallon banza,,"Na yafe,,tai
murmushi kan tace"Ok,ta juyo ga Hafeez, "Baby,bari na
wanke kwanika,.ya kada kai," Toh muje na Taya ki kwashe
wa,,Ta kallo Zahra,"No tnks, ka Taya 6s,.tai waje,. Tana
hawa sama tai kitchen ta kulle,kuka ta fara,tai ta wanke
fuska,ta dauraye kwanikan ta,,kan tai daki,,ta kwanta
bacci,kiran sallah ne ya tada ta,,ta tsaya gaban
madubi,Allah ya sota fuskar ta washe,,kai Kishi bala'i ne,Ya
Allah ka saukaka mana.
.
Yau sati guda,kai karar Zahra 3 wajen Hajiya,yau kam ta
kudiri musu zuwan ba zata,shi yasa ko Zahran bata sanar
wa ba..Da yamma ne,Lokacin kowacce na dakin ta,,
sallama tai,kan Zahra taji,,Da gudun ta ta fito,ta kan kame
ta,,Tace"Toh bari mu zauna tukun,Ta cika ta, Suka zauna
tana kallon ko'ina, a share amma ba kamshi,ba wari,,Ta
kallo ta lokacin da ta dakko Lemo,ta ajiye.,"kai Hajiya naji
dadin zuwan nan Allah,.
.
Ta zauna,chan tace "Au,.taje ta dakko cup,Sannan ta zauna
zaman gaisuwa,.Bata tashi ba sai da ta zube mata korafe
korafe sun fi a kirga, ita kanta sai da ta Gaji,,. Ta kallo ta,"
Rakani dakin yar uwar taki toh Zahra, ta bata rai,"Hajiya a
kira ta ta sauko man,.Tai murmushi, "Aa,bari itama naje
dai,.Sukai saman,,Ba ko kwankwasa wa Zahra ta ja glass
din,,Turus sukai,Lokacin da suka tarar tana rera kira'ar ta
mai zakin sauraro,cikin Suratul Yusuof,,earpiece ne a
kunnen ta, ya zame mata dabi'a karatun Qur'ani da safe da
yamma.,inkwa bata cikin tsarki,toh tana tare da Earpiece a
kunne ko ta kunna Mpn ta tana bi cikin nutsuwa, A jikin ta
taji kamar mutum a kanta,a firgice ta mike,,.Zahra ce tana
wani yatsina,sai Hajiya a gefen ta, Cikin fara'a ta cire
Earpiece din cikin nutsuwa,da tsabar girmamawa tace"
Sannu Da zuwa,.ta mike tare da nuna mata waje"Bissmillah,
Zahra sai harara take aika mata,,Hajiyan ta zauna,Zahra
ma ta zauna a kujera kusa da Hajiyan, ita a dole mai uwa a
gindin murhu,. "Ina wuni Hajiya?Fuska sake ta amsa
mata,Ina su Tasleem?.."
.
Tana Gaida ku,da tare zamu zo,,Ta dukar da kai cikin kunya
tana murmushi...Woo Sa'adatu BARIKI.. Tashi tai ta nufi
kitchen, sai gata dauke da flate da cups da ruwa da
lemo,,Tana zuwa ta durkushe gaban ta, da murmushi fal
fuskar ta, ta tsiyaya mata ruwa,ta tsiyaya lemo,Ta dau
lemon da girmamawa ta mika mata,. Cike da fara'a ta
karba," Sannu,,tai murmushi. Ta tsiyaya Tace"Sister ga
ruwa,,Ta tabe baki kan ta karba tana yatsina, duk Hajiyan
tana kula da su,,tasan kurba zata ajiye Sa'an ta karba da
sauri ta ajiye,,.shiru har yanxu Zahra ba taji an fara bam
bami ba,sai ma fadan da Hajiya ta musu dukan su,kan ta
tashi,,Sa'a Tace"Toh mun gode,a gaida su Tasleem,Tai
murmushi, "Zataji,. Suka fito ita kuma ta koma da sauri,.Har
sunje bakin mota ta karasa da dan saurin ta,..Tadan rissina
kadan," Hajiya,ta juyo,mika mata ledar, karba tai tana kallon
Sa'an, Tace"Ku gaida gida,Tace"Da wahala haka??Toh an
gode,Sa'an tai kasa da kai,,Hajiyan tai murmushi,"Allah ya
muku albarka,. Suna tafiya ta juya,Zahra ta dauro bayan
ta..
.
"Chusa kai ba kwarjini,,.Chak ta tsaya, kan ta juyo da
murmushi a leben ta, Hannu ta mika leben ta kan tai kissing
hannun ta nuna Sa'a dashi" Muahh,,Kan ta juya,Tuni ta kara
kuluwa,,"Karuwar kawai,,Ta daga mata kafada,,kan ta haye
saman ta tana kara bata haushi ta baya,,. Ta bita da
harara,ba abunda yafi kona mata rai sama da yadda kota
takale ta bata kulata,sai dai ma ta bita da wannan
murmushin da ta kira da munafuki,,. Yau watan su guda,duk
yadda Zahra taso taga sabani tsakanin su ta kasa,Sa'a ta
tsare gaba ta tsare baya,,.A ko yaushe Hafeez rawar kafa
yake akan ta,da girkin ta da ba nata ba,,.Sai dai yau da
Jummai tazo ta bata dabara,,girkin Sa'a ne, amma taci
uwar kwalliya da dogayen brown din nyty,,Yau tasan duk
tsiya sai Sa'a ta kwana kukan takaici,.
.
Tana jin horn din Motar Hafeez ta dan budo kofa,,ta fada
gado ta rike ciki,,yana shigo wa ta kwala ihu,,"Zan mutu
wayyo Mamy,,Dai dai Sa'a ta fito zata sakko tarar shi
kamar yadda ta saba,,da gudu yai dakin Zahra,, tam ta
tamke ido tare da rike ciki,, Ita Wai mutuwa zatai ya kai ta
gida,,Turus Sa'a tai,.Kai da gani kasan karya ne,,amma shi
ina,ya rude da jin tana ambatar mutuwa,,Da sauri Sa'an ta
karasa,tare da kamo Zahran"Sannu sis,Cikin ne??..Hafeez
ya kallo Sa'an, "Unique dan rike ta na kira Dr Seuss, Da
sauri ta rukunkumo shi,," Nidai kar ka tafi,.zan mutu,,...
.
Kut...Humm humm,.Lalle,Turnuku kenan,Wai Fadan
Ibilisai,,Yaro bai ga ba,bare ya raba,Sa'a ta kan kance ido ta
ciki,Lalle Zahra bata San wace ni ba??..Amma yau,zan fara
ware mata True colour na Wallahi, Daure wa tai bata nuna
musu ba,sai ma sannu da take ta kwararo mata ba
adadi,,Sune har 9,amma dai dai da second,zahra bata daina
kururuwa ba..shifa har ga Allah bai gano karya Zahra take
ba,dan tana da ciwan ciki,musamman lokacin period.
"Unique!.. Ta kallo shi, " Na'am Baby,,.Kije ki kwanta,in ya
ware zan taho,,ta kada mishi kai., "No Baby,,Kawai ka
kwana da ita,,Kaga ciwan nata,,Ya kalle ta zai magana tai
murmushi," It's Ok,,sis Allah baki lafiya,,Ta juya tana daga
mishi hannu,, Tafiya take da wani irin yana yi, sai yanzun
ya kula da kayan jikin ta,, Riga da wando ne yan
kanti,wandon Brown robber ne,ya dan bude ta kasa,sai rigar
mai net 2,Orange,ta baya tai zalolo,ta dame mata kugu,ta
gaba ta dage,,tai parking din gashin ta a tsakiya tare da
daura siririn gyale Orange,,Da kallo ya bita har ta rufe
kofa,,Ya lumshe ido,, Zahra ta na kallon shi,a ranta tana
"Yau kam sai gani daga nesa,.Ko minti 5 Sa'a batai da fita
ba ta ware,,tare da daura kan ta a kafar shi,,. Sa'a na shiga
daki tai wani murmushin mugun ta,, Tuni ta hau changing
kayan jikin ta.,''Zahra kinyi na kudin ki,,en my time start
now!!.. Ko'ina tabi ta kara fesa daddadan turaren ta,,ta
dawo daki ma haka,,Ta duba agogo 10 saura. Dube ta
fara,ta hango gwangwanin Air weak a mirror,,.. Tadi take
mishi,,tamkar ba ita ta gama ihun yanzu zata mutu ba,nufin
ta ta janye hankalin shi,sai dai ina, gaba daya shi hankalin
shi yana ga Unique Ladyn shi,dan tunda suke yau ya taba
ganin ta da English wears,, Murmushi yake yana kallon
kofar waje,ji yake kamar ana janshi sama wajen Sa'an shi..
Duk Zahra na kula dashi,Tuni ta mike a cinyar tashi ta fara
huci,," Wato har yanzun kwakwalwar shi naga Sa'a??
Gangar jikin shi ce kawai a nan??Tai kwafa tana kokarin
cire doguwar Rigar saman Suka ji an kwala ihu,,.A zabure
ya mike,kamar Sa'an shi yake ji fa??Zai waje Zahra ta tare
hanya,,"ina zaka kuma??Ya kallo ta yana kallon kofa,,"Bakiji
Kamar ihu bane a gidan??Ta maka mai harara,,"Ni banji
ba,,Yayi dai dai da lokacin da Sa'a ta kara sakar wani ihun
"Ahhhhhhhhhhhh....wayyo Allah... Inalillahi...
.
Da gudu ya fito, har yana tun tube,,itama Zahra ta biyo shi
da kira..a tsaye ya same ta a kan gado..daga ita sai wata
guntuwar rigar bacci pink,mai hannu siriri da breast cup,da
wandon ta iyakar shi cinyar ta, Shima kuma duk net ne,,da
gwangwanin air weak a hannun ta halamar zata daki wani
abu...da sauri ya karasa Shima ya Dane gadon,,tana ganin
haka ta kan kame shi,, " wayyo Baby,bera..bera ne..tana
nuna mishi bayan kofa..tamkar Zahra zata hadiyi zuciya
taji,,ita kam ta gamu da muguwar yar BARIKI,, ji tsinannun
kayan jikin ta??yanxu shikenan Kila ta wargaza mata plan..
Da ihu ta kwalla mishi kira,,suka saki juna suna kallon ta,,
Da sauri yace"Zahra ki shigo mu kwana a nan.,dan kinsan
wlh nima tsoron Bera nake,,.tuni ta fara hawayen bakin
ciki,ta juya zata tafi ya kira ta,.a zaton ta ko cewa zai
jirani,sai yace"Dan turo mana kofar please,,.ya wani marai
rai ce, Sa'a ta sau mata gwalo,tare da kashe mata ido
daya,Ta rungumo Hafeez din da wani salo,,Tuni gogan ya
sau ajiyar zuciya...kafa ta sa da masifa ta bige kofar,
"Bazan rufe ba,macuci kawai..Ina,shi bai ma san tana yi
ba,,Daki tai da gudu,sai kwa kofa ta tafi luuu ta rufe
kanta..Ya kara kan kamo ta,,." My Unique,. Love you,, Nan
ta biye mishi,sai da ta mantar bayanin bera kan ta zame
tace"After Dinner,.
.
Yau kam ta nuna mishi ainahin wace Sa'adatu BARIKI, Duk
wani abu da tasan zatai ta faran ta mishi a daran nan
tayi,,Sai da ta tabbatar babu wani gibi da yarage na nauyin
shi akan ta,,Hmm Sa'a Sa'a, Lalle she's Unique a wajen
shi,,. Fir Zahra taki fitowa Break,shikwa kamar jira yake
Suka kara yin sama bayan sun gama cika tankin su,,dan
yunwar cikin ta ta fito 12,ganan abinci a cikin flaks din ta,ba
kayan Sa'a ko 1,sai dai kofar glass din a bude tana Iya jiyo
dariyar da suke kyalkyala wa,,Tai kwafa,tana gama cin
abincin ta makawa Jummai kira,,"Banza kawai,wannan
dabarar taki banda ciwan zuciya ba abinda ta sa ni,,Jiya
kwanan kuka nayi,sai da nai Dana sanin aikata hakan
wallahi,, Daga chan Jummai tace "Ki jirani anjima kadan,,.
Sai bayan la'asar suka sakko kasa domin cin abinci,tana
kallo a parlour,da sauri ta dauke kanta,dan wannan fitsarar
bazata juri ganin ta ba,zuciyar ta zata Iya bugawa,a kujera
ya zauna,1 setter,hannun su rike da juna,Sa'an ta zauna a
hannun kujerar,, Ta kalle ta,," Sis,ya kwanan jikin??Ta maka
mata harara tare da sauya tasha ta manna mata,,ta kallo
Hafeez, "Baby,koh dai jikin ne ya dawo??Yai murmushi,"
Zahra bakya ji ne??Muna miki ya jiki..Ta kallo shi,, "Au jiki?
kasan da jikin ka barni ni kadai?,na mutu ko nai rai baka da
asara,, Yai kicin kicin"Ke Maintain fa,,Ina ce ware wa kikai
kina ta dirka firar ki,sai da na tabbatar kin warke kan na
tafi,.Baki sake take kallon shi, Dan haushi kasa masa
magana tai,,Sa'a tace, "Baby yunwa,,ta ruko hannun shi
tana marai rai ce fuska.." Oh sorry,.Muje,.Sun zauna ya
kallo Zahra, "Kizo muci man,ko ta dazu zaki mana??..Da
kamar kar ta tashi,sai dai kuma ta taso,,Sa'a tai serving
nasu,ta tura wa Zahra nata,su kuma ta zuba musu flate
d'aya,, A baki take bashi,shikwa Tuni ya kara narke wa
kamar yaro,,Zahra in banda chaka cokali ba abinda take
tana hararar su,,in ta bashi loma d'aya, sai ta kai loma
d'aya itama,tare da aika mishi murmushi,,. A haka har Suka
gama,abincin da Zahra bata ci ba kenan,,Kitchen din
Zahran Suka shiga,Suka kuskure bakin su,,yai ma Zahran
sallama kan zai fita shi kam,,sai da suka zo dai dai kofa,ta
dai dai ci Zahra na kallon su kan ta rungumo shi,," Ka kula
min da kan ka,tai mishi kiss a gefe gefen kumatun
shi,kamar irin larabawan nan,,shikwa sai yage baki yake,,
Zahra bata barke da lamarin ba,sai da ta ga Sa'an na wani
shagwabe fuska,,"Please Baby,,Come back soon,,U know
am gonna missed you..
.
Shikwa harda dan bubbuga bayan ta halamar lallashi,, Yana
"InshaAllah my Unique, Love you,,Yama manta da zahra na
wajen,,Ta cika shi tare da dan bashi light kiss a lips, tare da
goge bakin dan Jan baki ya taba" Love you too
Baby,,.Dakyar Suka ban bare yai waje,ina Zahra huci kawai
take,.Ta dawo daga rakiyar .. Tarar ta a tsaye tana
huci,,.Dariya ta fara harda rike ciki,,.Tuni Zahran ta kara
kuluwa..Ta rasa mey zata ce,sai cewa tai, "Karuwar
Kawai,,ai ba sai Kin nunan kin Iya BARIKI ba,dama nasan
da abar ki kika zo,,.ta harare ta tare da kama kugu.. Tako
wa tai tazo gaban ta,tare da dafa kafadar ta,,da sauri ta
zame hannun tana harar ta..Murmushi tai kan ta kada kai