Breaking News

HAUSA NOBLE'S

8.GANGAR JIKINSA NA AURA P8 NA (JUT)
Hanne tasake saka gefen
gyalenta ta share hawaye ta ce"Tun ina
shekara biyu ta rasu. Yaji gabansa yayanke
ya fadi ras, saboda yanzu ya gane Hanne
agidansu tana cikin halin wahala
kasancewarMahaifiyarta ta rasu da alama
kishiyar Uwa tana wahalar da ita. Allah Sarki
Hanne ya fada a ransayayin daya kura mata
ido. Hanne ta bashi tausayida, a yanzu kuma
ta sake kara bashi tausayi akantausayi
wanda badan ya daure ba da zai iyarushewa
da kuka. Can bayan sun dauki wani
lokacimai dan tsawo babu wanda ya sake
cewa komai. Dukkaninsu kansu a sunkuye a
kasa suna tunani,Haisam ya rike kai da
hannuwansa guda biyu canya dago ya kalli
Hanne ya ce "Yanzu dai a gidankuke kadai
Babarki ta haifa kenan baki da Yayye ko?
Hanne ta ce "Eh. Ya ce "Shine kuma ake saki
deboruwa kullum. Hanne ta ce "Ba debo
ruwa kawai ba kullum ni nake wanke-wanke,
shara, wankinsu, dakai dabbobi kiwo daga
can nayo musu ciyawa.Haisam ya buga kafa
a kasa ya ce "Kai wannanwanne rashin
imani ne haka? To ya akai kike
zuwamakaranta? Hanne ta ce "Sai wajen sha
dayan ranakoma wataran bana zuwa, tun
ana min dukan makaranta har suka daina su
Malamai. Shine waniMalami ya je ya sami
mai gari ya ce a yiwa Babanamagana a
dinga turoni makaranta da wuri tundaina da
kokari, Haisam ya ce "Sai da maigari ya
kiraBabanki ya fada masa sannan ake
turakimakarantar da wuri? Hanne ta ce
"Cafdijan shima Baban ya isa? Ya ce "Kamar
yaya bai isa ba.Ta ce "Shima tsoron Iya Abu
yake, matar tasazaginsa take,*ya*yanta suyi
masa, sai dai in ana dukana inakuka shima
yadinga yi. Hawaye ya sake kece mata,
shima ya jikwalla ta cika masa ido, ya dauko
wani hankici fari kal a aljihunsaya
gogeidanunsa ya mika mata, ya ce "Yi shiru
Hanne dainakukagoge hawayenki. Ta karba
ta goge. Haisam ya ce"Bari na danyi miki
tambayoyi naji kina kokari? What is
yourname?Hanne ta ce "My name is Hanne
Habu,Ya ce "Howold areyou? Ta ce "I'm
eleben years old. Wich school areyou? Ta ce
"I'm in Babban-mutum special primary
school.Haisam yayidariya ya ce "Hanne
Habu haka kike da kokari? Toke da
bakyazuwa makarantar sosai ya aka yi kika
koyi dukwannan? Hanne tayi murmushi ta ce
"Ai daga baya maigariyasa akakirawo ita iya
Abu da kanta taje fada ya sakashaidu ya
ce"Duk ranar data hanani zuwa makaranta
ko namakara sai ya kaita kara local
goverment. Sannan take barina
natafimakaranta da wuri sai dai idan na
dawo tayi tadukana tanacewa ga wanke-
wankenta nan harya bushe natsaya a hanya
ina wasa. Haisam yayi tsaki ya girgiza kai
alamartausayawa.Yayi gyaran murya ya ce
"Hanne ina so kiyi minalkawarin zakidage
kiyi karatu duk rintsi duk wuya. Kar ki zo
kifara ayi hutu ki koma gida kiga kawayenki
da yayyanki sunagida basa zuwamakaranta
kema kiki dawowa. Hanne ta
ce"Kwarankwatsazan dawo.(hahah.
Inkikayimata dariya bazancigabarmikiba,'Eh'
dake nake Zee )Haisam ya kece da dariya
(subhanallahi, tinda shima yayi to kema
danyi amma kadan),ya
ce"Kwarankwatsabarantsuwa bace wallahi
Allah za ki ce. Hanne tayidariya ta
ce"Mantawa nayi Malamin makarantar
Islamiyya yahana mu cewa kwarankwatsa.
Haisam ya ce "Kina zuwaIslamiyyakenan? Ta
ce "Eh, ada makarantar allo muke zuwadaga
bayaaka bude makarantar Islamiyya da
yamma dakuma dare duka ina zuwa.
Haisam ya ce dakyau Hanne yanzuidan
anyihutu kin koma gida sai kici gaba da
zuwa taIslamiyya karkifasa zuwafa kinji?
Hanne ta ce "To. Haisam ya cigaba da
kallonta har sai da Hanne ta fara jin kunyar
kallonda yakemata sannan yayi murmushi ya
ce "Hanne dukwannankwalliya ce kika yi a
fuskarki, ta zuwa makarantace? Hanne tayi
murmushi ta sunkuyar da kai kasa tana
rurrufefuska dahannu ta ce "A'a ba kwalliya
bace. Ya ce "Gashi nankinrambada kwalli
kinja wata doguwar jagira kinyifashin goshi
da kwalli kinyi digo-digo duk fuskarki kice
bakwalliya bace. Gawannan tsakiyoyi da kika
jifga a wuya da hannuhar kafarkima kin
daura, Yana dubanta yana dariya. Hannan
tace "Eh sarkar salla tace Baba ya siya mun.
Ya ce "Kingananmakarantar an hana sawa
idan Malamai suka ganizasu kwacesu
tsittsinka miki, ciro su ki bani in ajiye miki
saianyi hutu in zaki tafi gida na baki. Cikin
sauri taji zancentsittsinkawa taciro ta bashi,
yadda take bala'in kaunar sarkokinnan
natabata son abun da zaisa ta rasa su.
Haisam ya karbayana jujjuyasu yaga wasu
irin tsohon wuri ne aka jera sucikin liloaka
daura ya ce a ransa "*Yan kauye suna
gayu.Yayi murmushi ya jawo jakar kayansa
ya budewanikaramin zip ya zuba ya mayar
ya rufe. Ya juya yakalli Hanneya ce "Kuma a
cikin akwatin naki bude in gani kokinzo da
wani abunda dokar makaranta ta hana.
Hanne tatashi dagakan akwatin ta bude ya
karkato ya leka akwatinbabu abundaya
hango sai tsummokarai, cikin sauri ya ce
"Hanneme wancan nake hangowa kamar
miciji a cikinakwatinki? Hannetasa hannu ta
zaro wani dan siririn gyale baki
yakanannadeya kudindine ta ce "Gyale ne ba
miciji bane. Haisamya kyalkyale da dariya ya
ce "Na dauka kofi kika yiminna miciji.Hanne
ma tayi dariya ta ce "Gyale na ne dan
bansaruwa bana kadeshi shiyasa ya
cukuykuye, ya sake lekaakwatin sai ya
hango wani dan dogon karfe mai huda huda
ajikinsa, jikinsakamar farar azurfa yana
kyalli ya ce "Hannewannan fa,
karfenmenene? Dauko muga. Hanne ta yi
murmushi tadauko karfen ta mika masa ya
karba ya jujjuya bai san ko meyeba ya
ce"Wannan kuma na maye. Hanne ta ce
"Idan najekiwo nakeyiwa dabbobi busa
dashi, abun busa ne. Haisam yace abun
busa kuma? Hanne ta ce "Eh kawo ka gani.
Ta karbikarfen tamayar da akwatin ta rufe ta
koma kan akwatinta tazauna takaikaice ta
fara busawa Haisam wannan karfen kaikace
Sarkin busar Sarki ne yake yi, karin busar
mai dadi daalama daiwaka ce, Haisam ya
buda kunnuwa yana sauraroya baza idoyana
kallon yadda take yi.Can ta kyalkyale da
dariya ta ce "Haka nake yi.Haisam
yayimurmushi ya gyara zama ya ce "To ni
abunda bangane ba,kamar yaya sai kinje
kiwo kike yi? Daman a wajenkiwo ake yin
busa? Waye ya koya miki kuma? Nan da
nanHanne tacanja daga yanayin farin cikin
da fara'a da sakinjikin da takejikinta yayi
sanyi ranta ya baci. Haisam ya ce "Yakika
canja nan da nan daga tambayarki? Hanne ta
rushe dakuka ta kifakai da gwiwa, Haisam
yayi matukar mamaki daganin wannanhali
da Hanne ta fada yanzu-yanzun nan ya
ce"Yaya kina dariya ki koma kuka, Hanne
dago kanki. Ta dagoya ce "Gogehawayenki.
Ta goge. Ya ce "Fada min meye nakukan?
Hanneta ce "Wani abu na tuna shine ya sani
kuka. Haisamya ce "Meye abun da kika
tuna? Hanne ta sa hannu tasake
gogehawayen da ke idonta ta dauko abun
busar dakekan cinyartata rike a hannunta
tana jujjuya shi.Tace kullum dasafe nake fita
kiwo da raguna da akuyoyin iya abucan
dawa. Bana dawowa sai da yamma
musammanrabar asabar da lahadi. To
awajan kiwo ne nakehaduwa da wani tsoho
mai suna malam saleh. Wani lokaci sai yazo
ya wuce ni ina kuka idan yunwa tadameni
don yini nake anan kuma ba.a
kawominabinci. Har dai rannan ya zo ya
sameni a gingininuwa ina kuka. Yayi ta
tambayata dakyar dai nagaya masa yunwa
nake ji. yace '' ba.a kawo minabinci daga
gida ?nace ba.a kawomun kuma bana zuwa
dashi. Ya ce '' ina babata? Nace ta rasu''
shineya ce min kullum zai rinka bani abinci
ina ci dakekullum da rana daga gidansa ake
kawo masaabinci nan wajen kiwon rigarsu
tana nan kusakusa da garinmu , shine
kullum muke haduwadashi yana waka harya
koyamin nima nakoya. Sai ya ce ya barmin
abun busar tunda na iya, ko bayanransa
dansa zai ringa kawo shanunsa datumakinsa
kiwo na dinga yi musu busa. Bayan nannaga
kwana biyu naya zuwa kiwo bana
ganinshanunsa kuma. Hankalina ya tashi naji
duk banajin dadin kiwon ni kadai babu
wanda muke zama muyi hira muyi busa
muyi waka tare. Sai da akadade naga
shanunsa da tumakansa an kawosuwajen
kiwo amma ba malam saleh bane
wanisaurayi ne. Naji gabana yana ta faduwa
ko lafiyaina malam saleh yake? Naje na
tambayi yaron sai yace shi dansa ne kuma
babansa malam saleh satinsa biyu da
rasuwa shine a duk sanda naje kiwo
nagadabbobinsa sai suyi ta bani tausayi ina
kuka''hanne ta goge hawayen da yake zubo
mata haisamyayi ajiyar zuciya. Zuciyarsa
cike da tausayin hanneya ce a ransa'' hanne
yarinya karama tasan bacinrai, tasan tashin
hankali ta rasa kowa da zai tarairayeta
wanda zata gani taji dadi baya gamahaifinta.
Allah sarki , na yiwa allah alkawaribazan
kyale yarinyarnan taci gaba d tagaiyara
ba''ya juyo ya kalli hanne wacce har yanzu
take rike daabun busarta a hannunta tana
jujjuyawa.Yacekawo abun busar shima na
ajiye miki, idan ba haka shima malamai zasu
kwace'' hanne tayi murmushita mika masa
ya karba ya jujjuya ya bude zip dinjakarsa
inda ya saka tsakiyoyin nan nata ya saka
yamayar da zip din ya zuge ya ce'' yanzu
abunda za.ayi kije kicin gashi can ya nuna
mata da hannunsaya ce kice uwar biyu, tazo
inji malam haisam kinji ku taho tare'' hanne
ta mike cikin ladabi tana maiamsawa cikin
ladabi ta nufi inda ya nuna mata tanatafe
tana kara tsuke damarar data ci da gyale
akugunta.Haisam ya bita da kallo har ta kure
yayimurmushi ya girgiza kai'' bayan tafiyarta
da kamarminti biyar sai ga hanne da uwar
biyu sun taho tare bayan uwar biyu ta
gaishe da haisam durkuso harkasa duk da ta
haifeshi tama yi jika dashi amma
aidurkusama wada ba gajiyawa bace irin
abunalherin da haisam yake yi musu ita da
abokanaikinta na kicin sune masu dafawa
yan makarantaabinci. Duk ranar da yake
duty idan yazo kicin duk sai ya bisu da kudi
dukkaninsu don haka allahallah suke malam
haisam yazo kicin bayan sungaisa ya ce''
uwar biyu wata alfarma nake si kiyimin idan
baza ki takura ba '' uwar biyu ta sakegyara
gwiwoyinta da ta durkusa tace'' haba
malamhaisam menene ni kuwa a duniya
zaka nema ina dashi na takura ai babu sai
dai ma nayi murna yauharka nemi wani abu
a wajena , mai yi maka kansada kafarsa.
Kana yi mana alheri allah ne zai sakamaka
da alherinsa'' haisam yace '' amin na gode
.Ba wani abu bane daman wannan yarinyar
da kikagani kanwatace amma daga
kauyenmu taci makarantar nan babanta ya
kawota dazu. Tokasancewar acan basu iya
karatuba basu san ancea diko kayan
makaranta ba da sauran saye saye .To shine
naga dasu koma gida gashi garinbakusaba
shine nace zan baki ita ki tafi da itagidanki
kamar kwana biyu haka kafin na diko mata
kayan makaranta( uniform) da
sauransiyayya sai tazo ta koma hostel. Uwar
biyu tace''allah sarki malam haisam ai
wannan ba wani aikibane babu komai ai sai
mu tafi daman na gamadaure ledata tafiya
kawai zamu yi'' haisam ya ce'' tona gode ''
yasa hannu a aljihu ya dauko kudi ba tare
daya kirda ba ya mikawa uwar biyu yace ''
toga wannan don ku samu ku saisayi dan
abundababu'' uwar biyu ta karba zuciyarta
cike da farinciki da mamaki irin wannan
yawan kudin da koalbashinta na wata baikai
wannan haka ba, gashidaman wata yayi nisa.
Tayi ta godiya da da shi albarka har ya gaji
da amsawa. Ya kalli hanne yace'' hanne
inaga yau duk a wunin nan baki ci abinciba
ko? Hanne ta sunkuyar da kai tayi
murmushitace'' na karya da safe'' uwar biyu
tayi caraf tacea.a.a tin karin kumallon safe
kuna ta tafiya ko?Haisam yace nisa , don
haka uwar niyu kuje ki bata abinci taci ta
koshi.Haisam yace ki siya mata tsiren nan
na bakintasha dan alla '' uwar biyu tace to in
allah ya yardayanzu kuwa'' haisam yaci gaba
da cewa'' sannan kisai sabulun wanka da
mai me kamshi ki bata tayiwanka , karki
barta ta sharba yanxu duk fuskartata kwabe
da kwalli. Hanne ki daina yin wannan dige
digen kinji ? Hanne tace to uwar biyu
tayidariya tace'' ai da haka suma zasu zamo
'yan matasu koyi yadda ake kwalliya me
kyau irin na yanboko ko hanne? Haisam
yace'' ina ganin har kantasai an wanke , anyi
mata sabon kitso, ko kinyi kitsomuga kan?
Hanne ta zame dankwalinta ta durkuso da
kanta ta nuna musu wayyo allah kowa ya
kallikan hanne zai san bata da uwa a gidan
ko wanitsayayyen mafadi ko kuma kazamar
uwa allah yabata gashi ne irin
kanannadaddennan na fulani kobuzaye ko
larabawa mai laushi mai santsin gaskebaki
wullik mai tsawo sosai wanda yake taba
doron bayanta. Amma me ? Yayi datti. Kura,
amosalikai kace dambe tayi aka tumurmusa
kan a cikinyashi . Sai wani kitso tuma tuma
guda biyu dagagani ita tayi da kanta. Uwar
biyu tace'' la la hannehaka kanki yake ?
Amma kinyi wasa a yashi ko ?Gaki da gashi
tubar kalla baki san yan mata yanzu ido rufe
suke neman gashi ba. Da kudinsu ma
siyasuke su kara yaya kika bar kanki haka
babugyara ? Hanne tayi shiru kanta a
sunkuye a kasatana kokarin daura dan
kwalinta. Haisam wandayake zaune yayi
shiru sai girgiza kai alamantausayi. Can ya
nisa yace'' uwar biyu yanzu dai abunda za.a
yi ga wannan wasu kudi ne ya
sakecunkusowa daga aljihunsa ya mika mata
tace'' nameye wannan kuma? Ya ce'' ina
ganin hanne nabukatar abubuwa da yawa a
kwana biyu da zatayigidanki . Ki tsaya a
aishalle super market kitattambayi masu
wajen irin man wanke gashi, dana kitso da
sabulun wanka, wanki, abun goge kafa kisiya
mata silifas. Ki duba kan idan
akwaikwarkwata ki sayi shaltos duk a fesa
su mutu. Kozaki taho aiki gobe to ki sami
wata ki biya ta waccezata gyara mata
kannan tayi mata kitso. Kai harmawanka
kuyi mata da kanku ai bata wuce ayi mata
wankan bama'' uwar biyu tace'' in allah yaso
yaudin nan kafin mu kwanta da kaina zan
gyaratagobe kuma ko zan taho aiki da diyata
halima tananan auren ya mutu tana gida sai
in barta da ita.Kuma ta iya kitso kala kala
sana'arta kenan ki agarin da tayi aure''
haisam yace to nima gobe wajen karfe biyu
idan an tashi a makaranta akwai tela
dazamu je dashi can gidan naki ya auno ta
zai dinkamata kayan makaranta(uniform)sai
ki kwatantamin gidanki don naje. A kanti
kike ko cikin gari ?Uwar biyu tace'' ah a
cikin gari nake. Idan kajefada, kofar gidan
sarki daga hannunkan a dama zaka ga titi ya
mike to kabi shi kace a nuna makagidan
dalhatun kazaure alhaji hamisu to lyngun
mudaya ko a gidan kace gidan uwar biyu
kake nemayaro karami zai nuna maka dan
mu muke yi mususurfe, katangar gidanmu
daya'' haisam yace'' toshike nan yanzu k
dauki wannan kayan ku kai store din kicin ki
ajiye su sai nan da kwana biyuidan anyo
siyayya sai a dauko a zuba, sannankuma
abinda nake so dake bana son ki
gayawasauran abokan aikin ki ga dalilin da
yasa zata jegidanki da sauransu. Ko a cikin
gari ma kiyi gum dabakinki kinsan jama.a da
surutu za.a yi ta cewa an kawo yar kauye
makaranta babu komai sai dauwar biyu
takai gidanta wani malami ne yayi
matasiyayya da dai sauransu. Ba wai nace
kin cikasurutu ba ko gulma a'a ko mutum
daya yaji saidubu sunji. Kuma ai akwai
matan kicin da yawa damuke gaisawa amma
dana ga alamun suna da yawan magana ai
ban kira su na basu amana bako ? To yadda
tasa nace ta kira uwar biyu'' uwarbiyu ta
kyalkyale da dariya dadi ya lullubeta ''
tacehakane malam haisam ni dana ke
cikinsu yangulma ko sun tambayeni ni nasan
me zn fadamusu'' haisam yace'' yauwa ku
dauki akwati da bokiti da katifar kamar
yadda nace akai store aajiye, sai da safe''
suka ce allah ya kaimu''uwar biyuta kama
akwati ta dora akan hanne ta dauki bokiti,da
katifa a daya hannun suka doshi store din
kicininda suma suke boye shirginsu . Malam
haisamkuma ya rataya jakarsa ya nufi
gidajen malamai (staff qurters). Zuciyarsa
cike da tausayin yaddarayuwar hanne take.
Kuma da burin canza matanan gaba* * * *
HAISAM ABDULHAMID ZAKAR
Sunanmahaifinsa ne abdulhamid zakar.
Mahaifiyarsakuma sunanta NANA HAUWA'U
Wacce a yanzu akafi saninta da hajiya nana
ko kuma barista nana kasancewarta
kwararriyar lauya ce. Mahaifinhaisam
haifaffun unguwar kwalli ne a kano.
Kumasun fito daga tushe daya yar kanwace
aka hadasuaure a lokacin alhaji abdulhamid
ya gama karatumdigiri dinsa a london yana
da shekaru ashirin dabakwai ita kuma hajiya
nana ta gama karatun sakandire tana da
shekara goma sha shida.Dukkaninsu
iyayensu suna da matukar arziki. Donhaka
an sakar musu kudi yadda ya kamata
antafka musu kerarren gida, motoci an
kuma bawaalhaji abdulhamid jari mai tsoka
yana juyawa itakuma hajiya nana ta fara
karatunta na law a jami'a bayero ta kano.
Allah ya albarkacesu da ya'yahudu, uku
maza mace daya itace autar. Wacce ahalin
yanxu ko yaye ta ba ayi ba karama
ce.Babban shine yaya habib yanzu yana da
shekaratalatin , mai binsa shine abdulhamid
ake kiransa dahaisam yanzu yana
shekararsa ashirin da shida mai binsa
iziddeen shekarunsa ashirin da uku. Sai
daiziddeen ya gama sakandire ya shiga
jama'asannan aka yi masa kanwa mai
shekara daya anakiranta da amratu.Girma
yazowa alhaji abdulhamid da matarsaamma
kumakarfi ya tasamma ya'yansa zasu iya
kula da dimbindukiyarsada kamfanoninsa
yaya habib ya kammala digirinsaa jamia'ar
a.b.u ya karanta business admin a yanzu
yana aikia kamfaninbabansa shine kuma
mai zurga zurga zuwakasashe dabandaban
na shige da fice da kayan
kamfanonin.Haisam wanda a shekarar nan
ya kammala karatun jami'a yakaranta
bscgeography yanzu yana bautar kasa a
f.g.g.ckazaure da zararya gama kujerarsa ta
aiki nanan na jiransa a dayadaga cikin
kamfanonin mahaifinsa. Na uku wato
izziddenyana shekara tauku (level 3)a
jami'ar bayero ta kano yana karatunlaw don
yagaji mahaifiyarsa wato barista nana wacce
itacebabbar lauyar kamfanonin . Tana kuma
farin cikin ganin dayadaga cikin'ya'yanta ya
taso gadan gadan da karatun lawwanda a
cikin'yan shekaru kalilan zai gama ya zama
cikakkenlauya ya canjeta alhaji abdulhamid
ya dankawa yaya habibragamaraiki ya koma
gida ya zauna yana hutawa sai
daiyajekamfanonin fisha yaga yadda aiki
yake tafiya yakoma gida.Dan lelen abba da
umma wato haisam shine
yafikowashagwaba a gidansu ko kuma nace
shi akafishagwabawa tunyana kankani.
Amma ai izidden ne yakamata yayishagwaba
kasancewarsa ya dade yana auta kafin ayi
masakanwa ammashi yana gefe tun suna
yara haisam ne a kancinyarsabodatsananin
biyayya, ladabi , tausayi da jinkai irin
nahaisam shine ya kara masa fada a wajen
mahaifansa sunfisha'awarsu zauna suyi hira
da haisam sau dubu da suyi fayayansahabib
tun suna yara saboda haisam yake magana
acikin nutsuwa yake kalamansa masu
muhimmanci akoda yaushefuskarsa cike da
annuri(fara'a),wasa da dariya damanya
dayara. Bashi da raini ga hakuri , baya ga
zunzurutunkokari da allah ya bashi a
bangaren karatunsa dukka akur'ani da
bokonyasan alkur'ani kamar me a kansa duk
gidansubabu maiiliminsa. Hatta mahaifinsa
yakan yi masa tambayoyiakan duk wata
matsalarsu ta addini ko ta zamani, yana
datsananinhakuri sau tari ana masa abu da
yawa yayi hakuri.Ammakuma duk gidansu
babu mai zuciya kamarsa idanaka kureshi,
idan yayi fushi abin babu kyau mai hakuri
bai iyabacin rai ba.Da farko a enugu state
aka turashi bautar kasa(n.y.s.c)kasancewar
shakuwa da sabon da mahaifinsasuka yi
dashi basa so yayi musu nisa don haka
alhaji abdulhamidyasa adawo dashi kurkusa
saboda yasan manya manyakasar nandaga
yan boko har rukakkun yan kasuwa.
Ammaduk da haka haisam yana korafi shifa
kazaure yayi nisa da kanoa dawodashi cikin
kano inda kullum zaina kwana gida, dakyar
dai akalallasheshi yayi hakuri duka duka
bazai yi shekaradaya ba zai gama ya dawo
gida gaba daya. Don haka dukjuma'a
yaketafiya gida wani lokaci ma a kanon yake
yin sallarjuma'a sailahadi da yamma ake
dawo wa dashi. Gashi yanzuma baifi saura
wata uku ba ya kare bautar kasa
kwatakwata ma yakoma daya ke
muradi.Bayan tafiyar hanne gidan uwar biyu
da kwanauku wato ranar laraba da sassafe
sai ga wata mota an kawo
hannemakarantahaisam ya roki wani
abokinsa safiyanu yaje cangidan uwarbiyu
ya dauko hanne da kayanta ya
kawotamakaranta. Haisam ya gama mata
siyayyarta kakaf ko
yaranattajiranmakarantar baza su fita kaya
ba(provision)kayanmakarantarta
(uniform)suma har kala kala bibiyuyayi
matatakalma kuwa kala kala akwai kito,
sandal , kambos fari dabaki tsadaddu, silifas
dan madina har biyu, ya suyomata dawasu
yan kanti riga da siket suma kala biyu.
Yasuyo matajakar zuba kaya mai kyan gaske
yar madaidaiciya wato(travelling bag)a ciki
aka zubawa hanne kayansawarta, nata nada
kuwa yana gidan uwar biyu, kayan tande
tandedamakulashe kuwa abun baya
lissafuwa kama daga biskit kalakala, alewa
(chocolate)indomie, madara, milo,sugar
,complakes da dai sauransu ko gari
babuballe wanikanzo irin na yan makaranta
makilin da brushhadaddu, mayukan shafawa
da sabulansu masu kamshi gamayukangashi
cike a akwatin hanne hankar da kaya allahya
taimaketasa kansilansu ya tashi kawo maya
akwatin yakawo mata randimemiya, mai cin
kaya da yawa.Hanne sanye take da kayan
makaranta(uniform)kafar ta kumafarin
kambos ne da farar safa an tufke kitson
kantada waniribom mai kyau mai fulawa,
duk wanda yaga hanne kwanakibiyu da suka
wuce a yau dai bazai gane taba tayifari
kyalkamar yar larabawa, ashe mai dangwali
ya ba neda bakinkwalli suka cabe mata
fuska tayi baki kirin. Safiyanu yazobakin
offishin malamai ya tsaya da motarsa
sannanya fitodaga ciki ya juya ya kalli hanne
wacce ke zaune abaya tanakokawa da
murfin kofa ta kasa budewa abunka fa
bakauyiiya.Wannan ne karo na farko da
hanne ta taba hawadon hakabata san ina
zata ja kofa ta bude ba. Safiyanu yazagayo
dasauri ya bude mata, ta fito yace'' to dauko
jakar litattafan nakimana'' hanne tasa hannu
ta jawo wata bakar jaka(schoolbag)tsadadda
mai kyan gaske, yar
madaidaiciyadaidaibayanta cike take da
kitattafan rubutu da litattafan karatu
(textbook)duk dai kamar yadda aka zano
ajikintakardar babuwanda haisam bai siya
mata ba ga biruka da fensirdamathematical
set din su ya suya mata . Safiyanu ya
nunawahanne yadda zaya rinka ratayawa a
bayanta tarataya sukanufi cikin ofishin. Suna
shiga suka iske wani malamibayansafiyanu
ya mika masa hannu sun gaisa sai yayi
masa bayaninabunda ke tafe dasu yace
daliba ya kawo, sai yanuna masaofishin vice
principal yace nan zasu shiga.sukayi sallama
suka shiga suka iske viceprincipal
yanaharhada wasu takardu a gabansa, bayan
syn gaisasafiyanu yashaida masa cewa
yarinya ya kawo yar aji daya cesabuwar
zuwa sai ya nemi daya bashi takardar
shaidar cewaita dalibarnan makarantar ce
wato(joining instruction)daman haisam
yabashi ya dauko ya mika masa ya duba
yace''sunanta hanne habu imamu daga
babban mutum ko ? Safiyanuyace ''eh,''vice
principal din nan ya kurawa hanne ido
yanakallozuciyarsa cike da mamaki ga
yarinya kyakykyawakamar baturiya gashin
kanta har baya amma duk dama
antufkemata da ribon amma kuma sunnan
kauyawagareta gata kumadaa kauye. Ya ce a
ransa'' wata kila dai asalin garinsune babban
mutum din amma daga birni take, can
yanisa yace''babu komai,'' ya jawo wani
littafin rasitai ya budeyace dasafiyanu'' sai
ku bibbiya kudaden in baku rasitai dasauri
don yanxu lokaacin assembly ne, don taje ta
shiga cikindalibai ayida ita. Vice principal ya
lissafawa safiyanu yawankudade dazai kawo
safiyanu ya dauko ya bashi, shi kumayana
rubuta rasitai har ya biya kudin komai ya ce
'' sannan yafadi sunandakin da zata je,
sannan zata je j.s.s. 1A ajin
malamhaisamsunan ajin, yanzu ka kaita hall
ayi assembly da ita,kayanta kuma a barsu a
nan bakin staff room ana tashi tazozamu
samaigadi da prefect din dakin suje ta bata
gado.Safiyanu ya ce''to'' yayi godiya suka
fito yana sake yiwa hannebayani akan
abinda vice principal ya ce, yana kuma
karalallashinta ganinyadda nan da nan ta
canja hankalinta yayimummunan tashidaga
shigar su ofishin vice principal duk kwalla
tacika mata ido saura kiris ta fashe da kuka.
Yace mata'' kar kiyikuka nanmakaranta ce
karatu kawai za.a koya miki babumai
zaginkiballe duka kinji. Gashi ajin malam
haisam za,a kai kidon haka baki da matsala
zai kula dake''suna tsaye a bakin baranda
yana yi mata nasihasaiga viceprincipal ya
fito daga ofishinsa zai tafi hall
wajenassemblyyace'' ah har yanzu bata tafi
assembly ba ai gara kuyi sallamata tafi,''
safiyanu yace '' aima shikenan mun
gamadaman halldin zan tambaya don bamu
ganshi ba,'' viceprincipal t harcikin hall din
yashige da hanne a lokacin principal tana
bayanihall din yayi tsit kowa yana sauraro.
Amma dagashigowarhanne da vice principal
sai kowa hankalinsa yakoma ga
kallonhanne. Hanne ta zama yarinya ''yar
dagwas 'yar karama maikyan gaske akwai
dubbunan dalibai a makarantardaga
jahohidaban daban amma babu mai kyawun
hanne watokamarwata tauraruwa ce mai
haske a cikin taurari. Sai sheki take danfarar
fatarta hanci har baka, dan karamin
baki,gazar gazargashin gira dana ido fatar
jikinta luwai luwai irintayan hutuamma ita
dai daga innallahi. Ga ido dara dara bata da
kibakuma bata cika tsaho sosai ba gata
dirarriya duk dadaikarama ce masassakin
budurci bai fara sassakataba. Wasukitso ne
yiri yiri aka yarfa mata kamar bada hannu
aka yisuba. Hanne tayi kyau kwarai da gaske
a cikinkayanmakarantar nan ga 'yar jakar
litattafanta a baya.Babu wandazai kalli
hanne bai sake juyowa ya kalli halittar
ubangiji ba.Dalibai manyansu da yaransu
babu wacce bata cedama nicewannan ba ko
kuma ace 'yata ce a ransu ba.
Hattahaisamwanda ke tsaye a bakin kofa bai
gane hanne ba. Suka zo sukawuce ta
gabansa ya bita da kallo sai dai a
zuciyarsayaketambayar kansa da kansa ina
nasan wannanyarinyar?Tabbasa na santa a
wani waje, sai daga baya zuciya ta
bashiamsar cewa wannan itace hanne habu
kenan. Yayimatukarmamaki ganin yadda
hanne ta koma haka a kwanabiyu,hanne ta
tsorata ta kuma rikirkice ganin dubbunnan
idanuwacaa a kanta, ta tsaya cak, ta kasa
tafiya tana shirinfashewa dakuka.Vice
principal yayi kiran wata prefect dake tsaye
agefe yace tazo ta kaita layin 'yan j,s,s 1A.
Tazo ta kamahannun hanne takaita layin
ajinsu ana ci gaba da assembly kamaryadda
sukasaba. Bayan principal ta gama
jawabinta, viceprincipal ma ya fadi
albarkacin bakinsa sai aka nemi
sauranmalamai sucewani abu akan dokar
makaranta. Bayan sun gamaaka yinatsonal
pledge kowa ya kama gabansa, ya nufiajinsu.
Hanne ta tsaya cak a inda take tsaye tana
kallon dalibaikowa yanatafiya ajinsa ta rasa
ina zata nufa. Haisam ya matsokusa da itaya
ce'' hanne yaya kika tsaya bakya gani kowa
yanufi ajinsu ke kika tsaya idan baki sani ba,
ba sai ki tambaya ba.To nanmakaranta ce
kowa ta kansa yake, gara ki rinkatambayar
dukabinda baki sani ba, muje in nuna miki
ajinnaku, hanne tace'' to'' ta bishi suka
doshi bangaren da ajujuwa sukeyaci gaba
dayi mata nasihohi akan kada ta sake ta
zamawawuya, idan bahaka ba sai sauran
dalibai su raina mata wayo tazama duk
abunda bata sani ba ta tambaya musamman
idanmalamiyana darasi idan bata ganeba
tayi masa tambaya.Hanne nasauraro da
alama kuma nasihohin suna shigarta.Haisam
ya kalleta yayi dariya ya ce'' hanne ince kin
zamacikakkiyardaliba babu wannan
damarar? Hanne ta kyalkyaleda
dariyahaisam yace'' to tunda kin zama yar
birni 'yar bokomai aji to yanzu komai naki
yzai koma na aji, kin san abundanake nufi?
Hanne tace ''a'a'' yace to sunanki zai tashi
dagaHANNE HABUIMAMU ZAI KOMA
HANNAH ABUBAKAR IMAM.kowaya
tambayeki sunanki kice..'' kafin ya fada cikin
murnada farinciki tace '' hannah abubakar
imam'' haisam yatuntsire dadariya yace
harma kin rike sunan kenan? Hannetace eh
hannah yafi dadi Allah'' a daidai wannan
lokacisuka haubarandar ajin haisam ya wuce
gaba ya shiga ajinhannah nabiye dashi a
bayasuka shiga dukkan daliban ajin suka
mike dongirmama malaminsu suka hada
baki dukkansu''good morning sir'' haisam
yayi murmushi yace''morning how are you ?
Suka sake hada bakisuka ce'' we are fine
sir'' yace thank you sit down ''kowacce ta
zauna akan kujerarta. Haisam ya jawo
hannah gaban aji yace'' ga wata sabuwar
dalibakun samu'' rauda itace monita ta mike
tace'' lah ,what is your name ? Hannah ta
daga ido tanakallon haisam'' ya harareta
ma'ana ta bada amsa ,hannah tace'' my
name is hannah abubakar imam''kama
yadda haisam yace ta dinga fada. Nusaiba
wacce itace mataimakiyan monita tace''
emh, nicename you are welcome hannah''
haisam yayimurmushi ya ce'' kun fara iyayin
naku ko ? To mazaku saka mata kujerarta a
tsakiyar taku a gabakuma kunga itama yar
kucila ce kamar ku'' cikinsauri rauda taje
bayan aji ta dauko kujera ta kawo ta koma
ta dauko tebur yazo ta dasa a tsakiyar su
ajere. Dake duk ajin su duka ukun sune
kanananajin sunfi kowa kankanta
kasancewar akwaidingin dingin din yammata
a ajin musammankabilun na wata sai ka
rantse uwa ce amma yar ajidaya ce farin ciki
ya lullube hannah da haisam musamman ma
haisam yaga hannah ta samu shigaa wajen
nusaiba da rauda wadanda su suka fi
dukyan ajin kokari dan rauda a america tayi
karatunnusery da primary dinta don haka
tana bala'inkokari ga turanci daya kama
bakinta hausa matana kokarin ta subuce
mata.Kuma auwal abokin haisam ne na
kuttan kaibabanta alhaji shitu abokin baban
haisam nesannan ramla yayarta ita haisam
zai aura don hakanema aka kawo rauda
makarantar saboda haisamyana nan tazo
akayi mata jarabawa taci shikenanaka
dauketa, don haka nema take kiransa da
yaya haisam sabanin uncle haisam da
sauran dalibaisuke kiransa. Nusaiba ma
wata tsadaddiyarmakaranta ta gama a abuja,
ita yanzu hakaiyayenta suna abuja karatu ya
kawota nan ammasu haifaffun garin
gwambe ne fulani, rauda danusaiba sun
zama kawaye tun ranan da suka hadu ranar
da aka kawosu makaranta, ajinsu daya
sukakuma ci sa.a dakinsu daya don haka ga
gadonrauda ga na nusaiba kuma sun hada
kayanakwatinsu. Haisam yace monita da
mataimakiyartaku biyoni waje ina da
magana daku rauda danusaiba suka mike
suka bi haisam wajen ajin. Hannah na zaune
babu abunda take sai kallonginin ajin da
dalibai daya bayan daya taga kowaccesanye
da uniform dinta tsaf tsaf, fararen
takalmakambas da fararen safa kan
kowacce kitso ne tar.Hannah tace a ranta
ashe da na sha kunya da aceranar da baba
ya kawo ni a haka na shigo ajin nan da na
fita daban, kai wannan malami ya
taimakeniallah yayi masa albarka. Taci gaba
da kallon gininajin da irin zane zane da akayi
a takarda duk anlillika a jikin bango ga
fankoki a jikin silin sunatafitar da sansanyar
iska suka , ginin bulo hannah tafada a fili ba
tare data san a baiyane ta fada ba, bayan
fitarsu haisam a bayan ajin suka tsaya
yakalli rauda ya juya ya kalli nusaiba yace
raudanusaiba su duka suka amsa yaci gaba
da cewa gahannah nan , kamar rauda kike
kawar nusaiba tohannah ta zama kawarki
itama, sannan kamaryadda ke nusaiba kike
kawar kawar rauda to ina son hannah ta
zama kawarki duk da ku biyudakinku daya
to hannah ma yar dakin kuce dakesafiyanu
ya fada masa sunan dakin hannah yacedon
haka ku uku dakinku daya ajinku daya.
Kamaryadda a ko ina kuna tare a hall ne, a
ajine a daki neto hannah ma ta zamana
kuna tare itama kanwata ce kunji ko ? Su
dukka suka amsa. Nusaiba tace''uncle
haisam ko baka ce mu zama kawaye
badaman zamu zama tana burgemu'' haisam
yayidariya ya juya ya kalli rauda yace''
kanwata ke bakice komai ba ke bata
burgeki ? Rauda ta tabe bakitace'' yaya
haisam rannan fa kace nice kadai kanwarka
a makarantar nan yanzu kuma kace itace''
haisam ya kyalkyale da dariya ya dafa
kantayace!! Rauda kenan, ai har yanzu kina
nan amatsayinki na kanwata itama hannah
yar uwata cekibga dole kanwatace, nusaiba
ma kanwata ce donhaka karki damu. Gata
nan duk abunda bata sani ba akan karatu ki
koya mata. Haka kuma maganada turanci ku
rika tunasar da ita koda ta manta tayihausa
karku rubuta sunanta a masu yin hausa sai
ahankali zata saba itama ta rinka yin turanci
sosai.Haka a daki idan bata san yadda zata
yi amfani dawani abu ba kamar man gashi in
zata shafa a jiki ku nuna mata mata na gashi
ne ba ku ringa yi matadariya ba kuna
gayawa kawayenku kunji ?Musamman ke
rauda kinga rose suna yawan kawomun
kararki wai kina yi musu tsawa kar in
sakenaji kina yiwa hannah kinji ko ? Rauda
tace''yayaya za'ayi ta shafa man gashi a jiki
sai kace bakauyiya'' haisam ya ce a,a wai a
misalai nakenufi, koda ace zata manta ta
dauko man gashin''tafiyar wani malami ce
tasa duka hankalinsu yahuya baya don ganin
mai tahowa, haisam yace'' toshikenan ku
koma aji ga malam shaiya nan zaikaya
muku maths an kada firs period,'' suka ruga
a guje, malam shaiya ya mikawa haisam
hannu sukagaisa sannan ya nufi s.s.3c yana
da period yanakoya musu geograpykamar
haisam yayi duba da yace idan ta daukoman
gashi zata shafa a jiki haka kuwa aka
yihannah babu abunda ta sani a kayan
akwatintadaga ta dauko man wanke gashi
[shamppoo] takwaba a jikinta sai ta dauko
man shafawa ta makaa kanta makilin ma
wani lokaci a tsagar kitso rauda tazo ta
isketa tana sharbawa. Suyi ta dariya har
sugodewa allah daga karshe dai suyi mata
bayanidalla dalla , wannan ne na kaza
wannan kuma awaje kaza ake shafawa.
Babu laifi a sati biyuhannah ta waye ta gane
duk kayayyakin amfani nazamani sannan ta
koyi cin kayan gwangwani dana kwali, don
da farko inda suka dama comflask
damadara cokali daya zatayi sai ta fita a
guje ta kelayaamai bata sanshi ba haka
sardine da gesha kifingwangwani sai taki ci
tace tsutsace amma dagabaya duk ta waye
tana ci. Hannah tana farin cikimatuka da
wannan sabuwar rayuwar data tsinci kanta.
Abinci lafiyayye a akwatinta na makaranta
,gashi tana cikin yara sa'anninta suyi karatu
taresuyi wasa tare musamman nusaiba tana
bala'inkaunar hannah tafi rauda kirki don
rauda ta cikanuna isa da nuna tafi kowa
kuma duk girmanka saita riga daka tsawa.Ta
fannin karatu kuwa. Ada hannah dumama
kujera take yi kawai saboda tsantsar turanci
ake yia makarantar amma sai nusaiba ta
lura hannahbata fahimta don haka a koda
yaushe bayanmalami ya gama darasinsa sai
ta matso da kujerartahar kusa da ta hannah
tayi mata bayani dalla dalla. Haka shima
malam haisam kullum a prep dinyamma
yana zuwa ya kira hannah ya koya
mataabubuwa da dama. A wata daya hannah
ta faragane turanci fiye da yadda kuke zato.
Ranar wataasabar da daddare ranar ne ake
warewa dalibai sushakata su hole rayuwarsu
kamar a saka musu kidan disko su cashe
wasu kuma su kada tebur dakansu suna
waka wasu na rawa. Wasu kumatalabijin ake
kunnawa da bidiyo suyi kallon kasetduk dai
abunda ransu keso shi zasu yi. Daga
'yanj.s.s 1 har manyansu s.s.3