Breaking News

*** *BARIKI IYAWA PART 1* ***


*** *BARIKI IYAWA PART 1* ***
.
Na Feena Jaafar
.
Tafe take cikin tukun ta na masu isa,da takama,tamkar mai
gudun taka kasa,,hasken solar,kadai ke haskata da
walwalin net din jikin ta..duk wanda yaci karo da ita,,toh
koh ya tsaya kallon ta,, ko kuma ya wuce yana waiwayen
ta,,wata iriya ce ita.. Allah ya bata abu 3...
.
Kwarjini... Kyau,dan akwai zubii. Sannan uwa uba Aji.. Duk
ustazan cinka akaf unguwa da kewayen nan kasan da
zaman ta., sanye take cikin Riga da skirt na wani rantsatsan
farin net,da head blue, ta zuba wata uwar sarka ta Daham
kirar Dubai,,ga wane shegen takalmi mai tsinin tsiya
blue,.rike da karamar jakar ta blue,, sai katon net data rufa
blue a matsayin gyale,,in ka ganta,zaka rantse da Allah ko
wata yar shugaban kasar ce.. Ba yar Haj Ladi da Malam
Abdu ba..."BARIKI"kenan..wanda take wa kanta kirari da
"IYAWA. kai da ganin ta zaka gani wani take jira,domin tana
kallon agogon hannun ta tana dan tsuka,,fuskar nan sai
sheki take tasha make up tamkar wacce zata zaben
sarauniyar kyau..harara ta kwada mishi,lokacin da yai
parking din motar a gaban ta,, sanin hali yasa daga nesa ya
fara bata hakuri "Hajiya amini afuwa, wlh go slow na samu,
gashi mai goge motar ne aka kai Matar shi asibiti kuma ya
hana baya nan a bada...tsaki taja kanta warce mukullin
motar ta,," kai kana rasa karyar kare kanka ne..ji shi a
gun,,wlh na kusa sauya ka...kasan kwa yau ranar nan
yadda take a waje na??ya dukar da kai"Hajjaju ai hakuri..ta
bude pose din ta da bashi dubu1 "kaban waje..tuni ya kauce
ta shiga motar... Tana zama ta duba mudubin gaban motar,
ta Wai waiga cikin motar,kan ta bude ta dakko air freshener
ta feffesa.." Dan iska,duk ya loda min garadan banxa a
mota tana wari.. Tai tsaki,kan ta daura belt ta bata key..
Motar ma kamar bata so take Jan ta..wayan ta ne yai
kara..ta dauka,ita kanta wayan kasan ta manya ce.. "Haba
"BARIKI"... wulakancin da zaki min kenan??8 da kwata fa
yanxun... Da sauri ta katse ta" ee eehm...yi min a hankali..
Gani nan bisa hanya..tace"Dan ke muka maida abun nan fa
8,kowa yazo amma kujerar ki empty..sannan har yanxun..
Kit ta kashe wayan"jaraba..mutum sai mita ya tsohuwa.. Ta
sanya CD na wakar Ashique ta taka totur mota ta kara
gudu... 15 mint ya kaita harabar hotel din da zasuyi
program din,,tai parking kan ta fara takun nata na isa..waje
ya hargitse..tamkar wanda ake gidan bikin mata,don baa
gama zama ba,,da Zee ta fara karo da Royal...
.
Tuni suka hau mata kirarin da ita kadai suke wa a duk
qawaye.. "Yeee...kaga manya a Baku naku daban... Kaga
mai sai maza caroling mai sa mata su watse...kaga farar
mace..Alkyabba ta mata..wai sukari bakai farin banza
ba..tuni kanta ya fara fashe wa..dan mudin suka gamu da
da qawayen ta yan qarya.. Mai kirari ta cigaba..ita kwa sai
wani juyi take tana yatsina halamar mai tai lacking.."Dawus
u ce ke..ta kowa dole a kalle ki..in dake a waje dukkan
mata su kauce..Allah ja mana ran suka Sara mata tare da
cewa"BARIKI... Tuni tai wani fari tare da rausayar da kai ta
na kada keys..kan a hankali ta furta"IYAWA ba..ta barsu
nan tai chan ciki ta zauna kujerar kusa da amarya..suka
bita da kallo...tana kula da Yadda mutum 2 ke Binta da
harara .. amarya da abokin ango..ta kalle shi ta tabe baki
kan ta zauna.
.
Tamkar ita ake jira kuwa aka fara sanar da kowa ya zauna
a mazaunin shi.. Suka danyi bayanan su..tana ta kula da
har yanxun Harar da Hafeez yake mata.. Ta kada kai.. Lalle
ya kamata tai gaggawar saita mutumin nan.
.
Tunda take babu wanda ya taba kokarin shiga hancin ta sai
Hafeez,da kudundune ma ya shiga shi..tai kwafa dai dai
lokacin da aka tashi amarya da ango zasu yanka cake,
chan baya yai yadda shi kadai ne karshe,, a hankali itama
ta tako,tare da daukar kwalin 5alive tai wajen da yake..da
wannan takun nata, yana ganin ta ya kara hade rai,, tai
murmushin mugun ta, a dai dai shi ta tsaya kamar zata
gogi jikin shi,, yai tsaki,Yarinyar nan ba karamin tsanar halin
ta yai ba..tunda ya gano ita wacece... Yasan duk macen
kwarai bazata so a kirata da sunan BARIKI ba..yai tsaki tar