NA MANTA KOMAI Part 1
NA MANTA KOMAI Part 1
.
*****************
Alhaji Rabo....Alhaji Rabo....! Sunan da take ta k'ara
nanatawa a cikin ranta kenan, ta fa'di wannan Suna yafi a
k'irga, Mtswwwa..., sunan ko da'di babu. Sai zagaye
da'kinta take,ta kasa zaune ta kasa tsaye..., Ta K'ara le'ka
Window(Taga) d'in dakinta dake sama,ta hango mutane sai
kai da kawowa suke cikin harabar gidansu,daga cikin
runfunan da aka kafa kuwa na daurin aure har mutane sun
fara taruwa. lallai yau ake yinta,! "Yama za'ayi dady yamin
haka?,Ashe dama ba sona yake ba, ni kuwa duk rayuwata
babu wanda nake so duniya Kamar dadyn na." Wasu k'walla
masu zafi Suka gangaro daga idonta. "Yanzu ya za'ayi na
sulale nabar gidan kafin a d'aura auren nan ba tare da wani
ya ganni ba?" Wannan tunanin take yi a ranta,gashi aure
kam ba fashi, har mutane sun fara taruwa,lallai yau akwai
Masifa,Wasu qwalla masu zafi Suka gangaro daga idonta.
Tunanin ta da'ya yanda zata sulale tabar gidan kafin a
d'aura mata mugun auren nan..!
.
*** Kayan haushi! Ba d'an aike ba wanda ta aika a kira
mata.!Gashi lokaci sai k'ara k'urewa yake. A dai-dai lokacin
taji an yi knocking k'ofar d'akinta,tasan Yusuf ne ...dan
haka kai tsaye Tace "shigo"' gabanta na ta dakan uku-
uku.!! ,Saboda tunanin yaudarar da take shirin yi mishi.!
Duk da ba laifinta bane,Ba tare da ta kalli inda yake ba cikin
murya mai ban tausayi.., tace;" Yusuf yanzu kana ji kana
gani zaka bari ayi min haka,Dama duk da kake cewa kana
sona tun yarintarmu ba da gaske kake ba...." ta d'anyi shiru
jin bai ce komai ba yasa taci gaba da cewa; "to ni yanzu na
yanke shawarar kawai mu gudu dani dakai sai Muyi
aurenmu!! aurenka ya fiye mani auren wannan Alhaji Rabo
d'in. Tayi taku biyu zuwa uku tana kallon window tace; "
Alhajin da ban taba ganinshi ba bare har ayi zancen
aure,wallahi ga ra kai ko banza tare muka tashi,kuma nasan
kana so na ko?" Ta juyo ta kalleshi "kaga Daga baya mu
dawo bayan an daura aurenmu,babu mai iya rabani da kai a
lokacin...." Ta baro window ta tako ta tsaya dai- dai
gabanshi a inda yake tsaye tsakar d'aki,ta k'ara marairai
cewa ta ri'ko hannayenshi "Yusuf ni dama can ina
sonka,kawai nasan Dady ba zai yadda Muyi aure bane
shiyasa kaga bani biye ma harkarka wani lokaci, amma
wallahi inasonka, ko ka daina sona ne?"
.
K'walla Suka k'ara gangaro mata daga ido ta dora kanta a
kafa'darshi Ta bashi tausayi,duk duniya babu Abunda yake
So da K'auna irin Suhailah a rayuwarshi,ya d'ora hannunsa
a bayanta yana dan jijjigata,karo na farko da suka taba
ha'da jiki, duk da yaso yin hakan ba Sau daya ba amma
yasan bala'in da yake biyowa baya a duk lokacin da yaso
yin hakan saboda bata bashi dama,Yanzun ma yayi
hakanne dan ya San yayi mata na bankwanane,dan Ance
fad'an da baka iyawa,to ka Mayar dashi wasa.... Shi kam
babu yadda zayyi yaja da Alhaji Rabo....
.
Don ma batasan hardashi a yan ya'kin neman auren alhaji
rabo ba.Ina xaija da rabo wajen ya'kin auren Suhailarshi...y
a D'ago ta yayi mata murmushin k'arfin hali yace; "ya kike
So ayi yanzu?" duk da idonta yayi ja fuska ta kumbura sai
da ta yi d'an murmushi,ta sa bayan hannayenta ta goge
k'wallan dake zuba a idonta,tace " "Guduwa xamuyi, Xansa
hijabi har qasa Zan kuma yi yadda zanyi in fita ba tare da
wani ya ganni ba,sai mu tafi Sokoto gidan Anti Rukayyah
kafin su koma tunda suna nan bikina kaga sai Muje a daura
mana aure a wani masallaci. Yanzu ga wannan jakar da na
ha'da yan abubuwan da nake So ne,katafi da ita zan samu
a daidaita sahu da na fita gida sai ya kaini can gaba da
university, kai kuma sai ka daukeni acan. Hakan yayi!?"
Ka'da kai yayi alamar Eh,ya karbi y'ar k'aramar jakar da ta
mi'ko mishi yayi murmushi ya mi'ka hannu ya ri'kota yaso
yayi mata na bankwana,tayi baya da sauri ta watsa mashi
harara,Kamar yadda Suka saba a baya, ya fita yana fad'in
to sai mun ha'du....
.
Yusuf yana tafe yana mamaki, wai yau Suhailah ce har da
rungume shi. Lallai ya tabbata ba ta son wannan auren,
shida tunda yake sonta bata taba ba shi fuska ba, sai sama-
sama take kula shi, wai shine yau take cewa suyi aure
hadda su runguma. Abinda yasan ba zai taba yiwuwa ba,
koba komai ya ji dad'in rungumar shi da ta d'an yi,amma
yana bak'in cikin rabuwa da ita,wanda dama yasan ranar
na zuwa amma baiyi zaton ta nan kusa ba. Yana fita,
Suhailah tayi irin shigar da ta sabayi,wando da riga, ta
kawo hijabi data d'auko cikin kayan Antinta Rukayyah,
hijabin yakai mata har k'asa zunbulele dashi, ta sa cover
shoes flat (rufaffun takalma), yadda ba yadda za'ayi aji
sautin tafiyarta, ta k'arasa tattara 'yan abubuwan da dake
buk'ata ta saka a wata k'aramar jaka, ta jiyo wata yar
uwarsu tana "ina amaryar?" Tayi tsaki, "wai amarya, zaku
ga amarya ai," ta kashe wayarta ta jefa a hand bag (jakar
ratayawarta) dinta ta lallab'a ta fice ta baya ba tare da
kowa ya gantaba.
*********
Ta samu a daidaita ta shige. Sun wuce State University
(jami'ar Ummaru Musa) ta katsina da nisa sosai, sannan
tace ma dan adaidaita sahu ya sauke ta.. Ya ce "wallahi
hajiya dan kin birgeni yasa na kawo ki har nan gurin, amma
yadda k'asarnan ta lalace wallahi da sai nace ko ke yar
yankan kai ce cikin wannan uban hijabin haka, ke hajiya
gaskiyar magana kawai hajabin yafi kama da na mai dasa
bomb!!... Tayi murmushi, "wato masu hijabi sune yan
yankan kai ko da saka bomb?" Yace "sosai a Nigeria ma su
hijabi su ke saka bomb kuma kema kin sani sai dai idan
kink'i fada", tace Hmmm! Suna hakane dan su nisantar da
zukatan ya'yan musulmi daga saka hijabi, bayan hijabi
shine sutura ta mutuncin duk wata 'ya mace, kuma hijabi
umurnin Allah S.W.T ne, shi ya umurcecmu da mu rik'a
sakawa cikin Al Qur'ani suratul Ahzab ayata 53 (hamsin da
uku)... Yananan baro-baro ayar hijabi,so please ku daina
tsoron masu hijabi",...... Yace "Allahu Akbar, kawai mu dai
masu hijabi idan sun daina saka bomb to zamu daina
tsoron su". Dariya ya ba ta sosai,dan shi kam yana tsoron
masu babban hijabi...
.
Ta duba taga babu gida gaba babu baya, sai gaban ta ya
fadi. "hajiya wai mi zakiyi anan ke kadai?" Tayi murmushi
tace "kar ka damu wayanda za su daukeni yanzu nan za su
zo", dan ta lura yana shakkar ya barta a wajen.. Ta bashi
kud'i d'ubu biyu, nan da nan ya washe baki ya fara godiya
ya na sa mata albarka yaja kekenshi ya k'ara gaba. A
hak'ik'anin gaskiya Suhaila a tsorace take, ga rana na
dukanta, gashi babu ko 'yar bishiyar da zata labe a kusa,
motocin dake wucewa ma duk sun daina wucewa, ga
k'ishin ruwa ya dame ta, a ranta ta ce " lallai Yusuf ma ya
raina mani wayau". Ta kalli agogon hannunta, awarta biyu
tana jiran shi a inda mai a daidaita ya sauketa,ga yunwa ta
fara damunta, kenan awa biyu da rabi da d'aura aureta da
Alh. Rabo, ta k'lyalkyace da dariya, ita sunan ma ya daina
bata haushi, dariya yake bata. "Wai Alhaji Rabox", yau zaka
ga rashin rabo kuwa, dan guduwa xanyi, ta murgud'a baki
ita kad'ai. Ta kasa tsayuwa waje d'aya sai kai da komo
take. Ta sa k'afa ta harbe wani dutsi dake gabanta ta kuma
bi dutsen da kallo,d'aga idonta keda wuya sai ta hango
motarsa, tayi ajiyar zuciya cikin ran ta tace "sai yanzu dan
wulak'anci amma za ta rama," ta je inda ta aje kayanta a
gefen titi ta d'auko hijabin data aje da jakarta a dai-dai
lokacin da motar ta tsaya, bata ko kalle shi ba , ta jefa
jakarta a bayan motar,inda taga ya aje waccan jakar ta
dazu data bashi, ta bud'e gaba ta zauna,tayi kyacci tace
"haba Yusuf" sai kuma tayi shiru, Amma za ka sani, zan
rama da ni ka ke zancen, wai dan wulak'anci sai yanzu ka
ga damar zuwa ko?", yace "Eahhhhh".....
.
Jin murya da ba tayi zato ba,muryar da tun da ta ji ta ta
kasa samun natsuwa, yasa ta juya da k'arfi ta kalleshi, ta
bala'in jin tsoro,ta zaro Idanuwa! "Alhaji Rabo" tana tunanin
kai wannan mutumin dai ko aljani ne yake yi mata
wobuwa,ta juya inda ta aje jakarta,ta ga lallai jakar tace,
wadda taba Yusuf a wajen, so ina ya samo ta? Da k'arfi ta
bude k'ofar mota ta zuba aguje,gudu take iya k'arfinta tana
tunanin Allah yasa mafarki take, gudu take kamar me, kai ko
mafarki ne ta wahala cikin wannan mafarki, ya kamata ta
farka hakanan, ta juya taga inda tabar shi a motar ma bai
motsa ba, yana cikin mota abun shi zaune, ta juya taci gaba
da gudunta, kamar daga sama sai ta hango shanu sunyo
kanta, ta rasa yadda zatayi,sai kawai ta duk'e nan inda taja
birki,......
.
Haka suka yi ta wuceta har ta ji alamun sun gama wucewa
tayi ajiyar zuciya, ta mik'e tsaye, tashinta keda wuya sai
wani k'aton sa.. yasa k'ahonshi ya d'auketa ya wurgar da
ita kan titi ji kake timmm! Subhanallah! Ta sa ihu,amma
kamin ta kai k'asa dan olo har ta some. Ahmad yana
hangota, ya k'araso da sauri inda wannan k'aton san ya
wurga da Suhailah ya jijjigata amma yaga bata motsi, ya
dauke ta tsaf ya sakata mota, ganin ba bu wani ciwo jikinta
sai dan k'warzane a gwuiwar hannunta na haggu yasa bai
wani tad'a hankalinsa sosai ba, ya tada mota yaci gaba da
tafiyar shi ba tare da ya tsaya ko ina ba, ya d'an tausaya
mata ganin k'wallan da suka gangaro daga idonta... Koda
ya tsaya yasha mai a kaduna yaga ta ma gyara
kwanciyarta amma bata san abunda ake ba, sai ya k'ara
kwantar mata da kujerarta dan taji dadin bacci, ya kula
daga suma ta wuce bacci ne.
.
Daga nan bai tsaya ko inaba sai gidan gonar shi dake Abuja
chan hanyar keffi......